18 Agusta 2020 - 10:28
Ghana Ta Mikawa Kungiyar (AU) Ginin Sakatariyar AfCFTA

Kasar Ghana ta mikawa kungiyar tarayyar Afrika, ginin sakatariyar yarjejeniyar cinikayya marar shinge ta nahiyar.

ABNA24 : Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ne ya sanar da mika ginin sakatariyar ga kungiyar ta AU, yayin wani jawabi jiya Litini.

Yayin mika ginin, shugaba Akufo-Addo ya ce, kasarsa ta sauke dukkanin nauyin dake wuyanta, tana kuma aiwatar da dukkanin kudurorin da aka cimma tsakaninta da hukumar zartaswa ta kungiyar tarayyar Afirka.

Don haka ne ma a wannan lokaci ta gabatar da ginin sakatariyar AfCFTA, mai kunshe da dukkanin kayan aiki, a wuri mai tsaro da saukin zuwa, dake shiyyar hada-hadar kasuwanci ta birnin Accra.

Shugaban na Ghana ya ce kasarsa ta yi imanin cewa, karuwar hada-hadar cinikayya daya ne daga manyan hanyoyin zurfafa dunkulewar nahiyar Afirka.

Kaza lika hakan zai bunkasa musayar amfanin gona, da hajojin masana'antu, da hada-hadar kudade, da bunkasa binciken kimiyya, da albarkatun fasaha.

Tuni dai jagoran yarjejeniyar ta AfCFTA, kana kuma shugaban Jamhuriyar Nijar, Isufu Mahammadu, ya yabawa kasar ta Ghana akan cika wannan alkawari datayi.

A shafinsa na twitter, shugaba Isufu, ya ce, wannan shi ne ke nuna cewa kasar Ghana da gaske take kan ganin an aiwatar da yarjejeniyar ta ciniki marar shinge tsakanin kasashen na Afrika.

342/